Zidane: Kasancewar Messi a Spain na karawa gasar La Liga daraja

0 224

Mai horas da Real Madrid Zinaden Zidane ya shawarci kaftin din Barcelona Lionel Messi kan cewar zai fi kyau yayi ritaya a kungiyarsa, maimakon neman sauyin sheka kamar yadda aka rika alakanta shi da hakan a watannin baya bayan nan.

A cewar Zidane kasancewar Messi a Spain na karawa gasar La Liga daraja, dan haka kamata yayi ya hakura ya cigaba da zama da Barcelona.

Zidane ya baiwa Messi shawarar ce, a yayin da ake shirin karawa tsakanin Real Madrid da Barcelona a babban wasannan na El Clasicco a gasar La Liga.

Wasan na ranar asabar dai na da muhimmanci ga dukkanin kungiyoyin biyu dake a matsayin na biyu da na uku, da bambancin maki 2 tsakani, a yayin da suke hankoron doko Atletico Madrid daga zama jagorar gasar La Liga a kakar wasa ta bana.

Rabon da Messi ya jefa kwallo a ragar Real Madrid dai tun wasan da suka fafata a watan Mayu na shekarar 2018, abinda ke nufin ya fafata da kungiyar ta Real Madrid har sau 7 ba tare da ya jefa mata kwallo ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: