Zanga-zangar gama gari a kasar Iran dangane da karin farashin man fetur ta jawo kame mutane sama da 40
Zanga-zangar gama gari a kasar Iran dangane da karin farashin man fetur ta jawo kame mutane sama da 40, an kuma bayar da rahoton mutuwar wani jami’in dansanda guda, yayinda hukumomin kasar Iran suke gargadi dangane da mayar da martani kakkausa.
Masu zanga-zanga sun fita tituna a manyan biranen dake fadin kasar suna adawa da matakin gwamnati na kara farashin man.
Gwamnatin Iran wacce ke fama da tabarbarewar tattalin arziki, sanadiyyar takunkumin da kasar Amurka ta kakaba mata, ta bayyana cewa zata kara farashin man ranar Juma’a.
‘Yan kasar ta Iran sun fara fuskantar biyan kudin mai ninki 3, dayawa daga cikinsu sunyi kiran da a gaggauta janyen karin farashin, duk da barazanar karuwar tabarbarewar tattalin arziki tare da rage darajar kudin kasar zuwa rabi.
Kamfanin dillancin labarai na kasar ta Iran, ya bayar da rahoton cewa an kashe jami’in dansandan yayin arangama tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga a garin Kermansha.
Hukumar leken asiri ta kasar Iran tace zata dauki tsauraran matakai akan masu zanga-zangar dake lalata abubuwa.
Mutane dayawa basu samun damar shiga intanet tun bayan da zanga-zangar ta habaka a ranar Asabar da yamma.