An rufe jami’ar gwamnatin Jihar Ekiti da ke Ado-Ekiti, bisa zanga-zangar da daliban suka suka shirya na neman a sake duba kudin makaranta.
A yayin zanga-zangar, dalibai saun toshe babbar kofar makarantar inda suka hana dalibai da malamai shige da fice.
Daliban sun yi Allah-wadai dakain kudi na naira dubu 5 da aka kakabawa wanda suka yi jinkirin kudin makaranta, inda suka bayyana hakan a matsayin abin da ba za a lamunta ba da sauran matsaloli da makarantar ke fuskanta.
Tun da farko, mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Edward Olanipekun, ya amince da dakatar da ayyukan koyo da koyarwa a jami’ar har na tsawon makonni biyu daga jiya Litinin.
A nasa jawabin kakakin kungiyar dalabai Dotun Ogunsanya, ya ce abin damuwa kasancewar babu ababen more rayuwa da kayan aiki a makarantar, domin an shafe sama da shekaru biyar a ciki da wajen makatarantar ba tare da wutar lanyarki ba.
- Comments
- Facebook Comments