Zan samar da dokar da baci kan samar da ayyukan yi ga matasa da zarar an zabe ni a Gwamnan jihar Jigawa – Mustapha Lamido
Dan Takarar Gwamnan Jihar Jigawa na Jam’iyar PDP Mustapha Sule Lamido, ya bayyana cewa zai sanar da dokar da baci kan samar da ayyukan yi ga Matasa da zarar an zabe shi Gwamna a shekarar 2023.
Cikin wata sanar da ya rabawa manema labarai a yau, Mustapha Sule Lamido, ya ce gwamnatin sa zata mayar da hankali kan Sana’oin hannu da kuma fadada Noman zamani a Jihar Jigawa.
A cewarsa, samarwa matasa sana’oin hannu zai taimaka wajen bunkasar tattali arzikin Jigawa ta yadda zata yi gogayya da takwarorinta.
Haka kuma ya ce Gwamnatin sa zata bunkasa fannin cigaban fasahar sadarwa, da wasanni da kuma Nishadi.
Kazalika, ya nanata kudurin sa na ware kaso 30 cikin 100 na mukaman gwamnati ga Mata da tare da samar da shirin haihuwa kyauta, ilimin Mata kyauta.