Zan Iya Rasa Kujerata Daga Yanzu Zuwa Kowanne Lokaci In Ji – Jibrin Kofa

0 227

Ɗan majalisa mai wakiltar Ƙiru da Bebeji a zauren majalisar wakilan ƙasar nan, Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana cewa a shirye yake da ya bar zauren majalisar.

Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana hakan a shafinsa na tiwita inda ya bayyana cewa

“Daga yanzu zuwa kowanne lokaci zan fara neman aiki, na haɗa bayanin karatuna waje guda shin ko akwai wanda zai bani aiki?”

Wannan jawabin yana zuwa ne bayan da shugaban majalisar wakilai Mista Femi Gbajabiamila ya yi cikakken bayanin abin da ya sanya ba’a ga sunan Kofa a ƙunshin shugabannin kwamitocin majalisar ba.

“Bari in bayyana muku cewa Abdulmumin Jibrin Kofa ba wai baya cikin ƙunshin shugabancin kwamitocin majalisa ba ne, a’a yana cikin waɗanda su ka tsara yadda shugabancin ya kasance, kuma ya ƙi karɓar kowanne irin shugabancin kwamiti”

“Ya bayyana mana kudirinsa na barin zauren majalisar wakilai. Maganganun da na yi masa tare da sauran wasu daga cikin ƴan majalisa ne ya ba shi karfin gwiwar cigaba da zama a zauren majalisar”

Mista Femi ya ce Kofa yana son komawa jami’a ne domin ya cika burinsa na zama cikakken malamin jami’a.

“Yana buƙatar komawa jami’a domin cikar burinsa tare da mayar da hankali akan harkokin kasuwancinsa ko kuma ya riƙe wani muƙamin gwamnati domin hidimtawa al’umma”

Idan za’a iya tunawa dai Abdulmumin Jibrin Kofa ya yi takara a tutar jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2019, inda ya yi nasara akan abokin karawarsa Ali Datti Yako na jam’iyyar PDP da tazarar kuri’u 685. Sai dai kuma Ali Datti Yako ya ƙalubalanci nasarar da Kofa din ya samu a gaban Kuliya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: