‘Zan bude dukkan iyakokin Nijeriya bayan na lashe zabe a 2023’ -Atiku Abubakar
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ne zai lashe zaben 2023.
Tambuwal ya bayyana cewa Atiku zai sake bude iyakokin Nijeriya da gwamnatin Buhari ta rufe da zarar ya lashe zaben.
Tambuwal shine ke rike da mukamin Darakta Janar na Majalisar Kamfen din Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP na kasa (PCC).
Ya bayyana ra’ayin ne a ranar Asabar a taron yakin neman zaben jam’iyyar da aka gudanar a karamar hukumar Illela da ke Jihar Sakkwato.
Tambuwal ya tabbatarwa ‘yan Nijeriya cewa Atiku yana da kyawawan tsare-tsare a gare su da kasar.