Zamu hukunta wadanda suka kai hari a jihar Yobe – Tinubu

0 155

Shugabn kasa Bola Tinubu ya tabbatar wa al’ummar jihar Yobe cewa wadanda suka kai harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama za su fuskanci hukunci.

Shugaban kasar, a jiya, ya yi Allah-wadai da harin da aka kai ranar Lahadi a Mafa, a karamar hukumar Tarmuwa ta Jihar Yobe, a matsayin zalunci. 

Ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa za a gurfanar da wadanda suka kai harin da ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dama.

Shugaban a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar, ya jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan wannan mummunan lamari.

Idan  za a iya tunawa a ranar Lahadi da tagabata, an kashe mutane da dama bayan wasu da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne suka kai hari wani kauye a jihar, inda suka kona shaguna da gidaje.

05-09-2024 SAUDYYA/YOBE                       12NOON

A wani labarin mai alaka da wannan, Ofishin jakadancin Saudiyya a Nijeriya ya yi Allah-wadai da harin ta’addancin da aka kai kan al’ummar Mafa da ke karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe.

An rawaito cewa, wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun afkawa al’umma a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka kai harin da ya kai ga kashe dimbin mazauna garin Mafa.

Sanarwar wacce ta fito daga ofishin Jakadancin kasar, ta jaddada yadda Masarautar Saudiyya ke adawa da duk wani nau’in tashe-tashen hankula, ta’addanci, da tsattsauran ra’ayi, tare da jaddada aniyarta na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya.

Sannan ta mika sakon ta’aziyyar Masarautar tare da jajantawa iyalan wadanda lamarin ya shafa, al’ummar jihar Yobe da kuma gwamnatin tarayya.

Hukumomin tsaro sun ce, ana ci gaba da kokarin ceto wadanda suka bata sakamakon mummunan harin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: