Zamu aiwatar da dukkanin tsare-tsaren kasafin kudin jihar Zamfara na shekarar nan

0 245

Gwamnan jihar zamfara Dauda Lawal, ya bayar da tabbacin aiwatarda dukkanin tsare-tsaren kasafin kudin jihar na shekarar nan.

Gwamnan ya bayar da tabbacin ne a lokacin taron majalisar zartarwar jihar da ya gudana a Gusau babban Birnin Jihar.

A cikin wani bayani mai dauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Idris, ya bayyana cewa a wajen taron wanda gwamnan ya jagoranta an tattauna muhimman batutuwa da zasu kawo cigaba a jihar.

Yace gwamnatin jihar zata mayarda hankali akan ganin ta cimma muradan da ta sanya a gaba da kuma kaucewa kura-kuran da akayi a baya, musamman a bangarorin tsrao, ilimi, lafiya, da kuma abaaben more rayuwa da bunkasa tattalin arziki. Ya kuma kara da cewa gwamnatin jihar zata fito da shirye-shirye da kuma sabbin tsare-tsaren da zasu tallafi kasafin kudin jihar na wannan shekara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: