Zababben Gwamnan Jihar Kebbi Ya Yi Kira Ga Sarakunan Gargajiya A Jihar Da Su Guji Siyasa

0 157

Zababben gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya yi kira ga sarakunan gargajiya a jihar da su guji siyasa tare da marawa gwamnatinsa baya domin samun ci gaba.

Idris a lokacin da yake jawabi ga hakiman Aliero, Danwarai da sauran wadanda suka yi masa mubayi’ar Sallah a gidan gwamnati dake Birnin Kebbi ya ce kiran nasa ya zama wajibi saboda rawar da suke takawa wajen ci gaban jihar.

Ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da doka ta tanada domin ganin an kara jajircewa wajen tallafa wa sarakunan gargajiya a jihar. Tun da farko Hakimin Sabiyal, Alhaji Umar Dodo, ya ce sun je gidan gwamnati ne domin gaisuwar Sallah ga zababben gwamnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: