Za’a yiwa ‘yan mata allurar rigakafi da za ta taimaka musu wajen hana su kamuwa da cutar mahaifa
Gwamnatin tarayya ta samu allurar rigakafin cutar Polio sama da miliyan shida da kuma sauran kayayyaki don kaddamar da rigakafin ga ‘yan mata masu shekaru 9 zuwa 14 a ranar 24 ga Oktoba, da muke ciki.
Babban Darakta Hukumar Lafiya a matakin farko na kasa, Dakta Faisal Shuaib ne ya bayyana hakan a jiya Talata a taron manema labarai a Abuja, ya ce allurar rigakafin za ta taimaka wajen hana kamuwa da cutar mahaifa da kuma rage hadarin kamuwa da cutar kansar mahaifa.
Dr Faisal ya ce, A cikin watanni da suka gabata, Hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da sauran hukumomi, sun aiwatar da cikakken shiri na bullo da allurar rigakafin cutar ta sankarar mama
Dr Faisal ya kara da cewa an samu sama da allurai miliyan shida na rigakafin cutar da kayayyaki masu mahimmanci. Babbar daraktar hukumar kula da inganci abinci da magunguna ta kasa NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ta bayyana cewa hukumar ta himmatu wajen tabbatar da tsaro da ingancin allurar rigakafin cututtukan da ake kamuwa da su a kasar nan.