Za’a tantance matasa fiye da 3,600 da suka nemi aiki karkashin shirin J-agro

0 350

Gwamnatin jihar Jigawa zata gudanar da aikin tantance matasa fiye da dubu uku da dari shida da suka nemi aiki a matsayin malaman gona karkashin shirin j-agro.

Mai baiwa gwamna shawara kan noma dan riba, Alhaji Muhammad Idris Danzomo ya sanar da hakan ta cikin shirin Radio Jigawa na musamman

Yace za a tantance matasan ne da suka sami nasara a jarabawar da aka gudanar a wasu cibiyoyi hudu da aka ware daga ranar litinin zuwa laraba masu zuwa

Alhaji Muhammad Idris Danzomo ya kara da cewar za a tantance matasan a cibiyoyin da aka ware a garuruwan Gumel da Birnin Kudu da Kazaure da kuma Hadejia

Yana mai cewar da zarar sun kammala aikin tantancewar zasu nemi izinin gwamna Umar Namadi domin basu horo na sanin makamar aiki

Ana sa ran daukar malaman gona 1,420 aiki karkashin shirin j-agro a jihar Jigawa Da ya juya ga bangaren noman shinkafa na rani kuwa, Alhaji Muhammad Idris Danzomo yace tuni wani kamfani ya fara rijistar manoman shinkafa a fada

Leave a Reply

%d bloggers like this: