Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya tabbatar wa jam’iyyar cewa za a shawo kan matsalar cikin gida da ta kunno kai bayan sanarwar sabbin kwamitin ayyuka na kasa da kuma jami’an shiyya na jam’iyyar.
A karshen wata ganawa da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, wanda aka gudanar jiya a birnin tarayya Abuja, Ganduje ya shaidawa manema labarai cewa za a gyara duk wani sabanin da baraka dake tsakanin yan jam’iyyar.
Shugaban jam’iyyar APC ya kuma nuna kwarin guiwar da gwamnan Kogi zai iya baiwa jam’iyyar jihar a zaben gwamnan da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Bello ya jaddada amincewar sa ga shugabancin jam’iyyar, inda ya jaddada cewa APC za ta ci gaba da rike mulki a jihar.