Za’a sakewa fannin ilimin Tsangaya da Islamiyya fasali a jihar Bauchi

0 254

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad ya jaddada kudirin gwamnatin sa, na sakewa fannin ilimin Tsangaya da Islamiyya fasali domin samun karatu cikin sauki kuma mai inganci,da kuma saukakawa masu ruwa da tsaki gudanar da ayyukan su a fannin.

Gwamnan ya fadi haka yayin taron bita na kwanaki 2 da cibiyar wanzar da zaman lafiya ta addinin Islama ta shirya a Abuja, hadin gwiwa da ofishin matar gwamnar Jihar Hajiya Aisha Bala Muhammad.

Gwamnan ya bayyana tsarin da abinda ya dace domin gabatar da karatu bisa tsari mai kyau a makarantun Tsangaya da Islamiyyu, inda ya kara da cewa gwamnatin sa zata baiwa fannin ilimi fifiko.

Bala Muhammad ya bayyana cewa gwamnatin sa zata dauki dukkan matakan da suka dace, domin samar da damar da zata baiwa Yara suyi karatun Addini dana zamani. A nata jawabin, matar gwamnan Jihar ta Bauchi Hajiya Aisha Bala, tace wannan taro da aka shirya an tsara Samar da kayan aiki ga malaman makarantu, da kuma hanyoyin koyarwa dai-dai da karni na 21.

Leave a Reply

%d bloggers like this: