Za’a kawo karshen hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a Najeriya

0 296

Ma’aikatar bunkasa albarkatun kasa tayi gargadi ga masu hakar ma’adanai na ketare ba bisa ka’ida ba, wadanda ke daukar nauyin yan bindiga domin samun damar kawar da hanlakin hakumomi da daga kansu.

Ministan ma’aikatar Oladele Alake ya bayyana haka a wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar Alaba Balogun ya fitar jiya.

Alake yayi gargadin ne lokacin da tawagar hadakar kungiyar masu hakar ma’adanai ta yan Najeriya da China karkashin jagorancin shugaban kungiyar Dr Olugbenga Ajala suka kawo masa ziyara a ofishin ma’aikatar dake birnin tarayya Abuja.

Alake yace ma’aikatar ta himmatu domin samar da hakumomi da zasu kawo karshen hakar ma’adanai ba bisa kaida ba, tare da dukkan masu goya musu baya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: