Gwamnatin Tarayya ta amince da kashe naira biliyan 4.8 wajen yaƙi da yaɗuwar cutar HIV a ƙasar nan.
Wannan na daga cikin matsayar da aka cimma a taron majalisar zartarwa ta tarayya, inda gwamnatin ta sanar da ware fiye da dala biliyan ɗaya ga ɓangaren lafiyar ƙasar.
Gwamnatin ta ce wannan yana daga cikin manufofinta na inganta kiwon lafiya a matakin farko.
Ta ce ta tsara kashe kuɗaɗen ne a fannin ɗaukar ma’aikatan lafiya da bayar da horo gare su, domin samun ƙwarewa da kuma tabbatar da an bayar da kulawar da ta kamata don hana yaɗuwar cutar HIV din a sassan ƙasa.
A baya dai an riƙa bayyana damuwa game da sabbin tsare-tsaren da gwamnatin shugaban Amurka, Donald Trump ta ɓullo da su, musamman a fannin bayar da tallafi, inda ake tunanin za su iya shafar tallafi ga yaƙi da cutar HIV a ƙasashe masu tasowa.
Amma a ranar Asabar gwamnatin Amurkan ta sanar da ware sabon ƙunshin tallafin yaƙi da cutar ta HIV.
Alƙalumman da hukumar hana yaɗuwar cutar HIV a Najeriya ta fitar, sun ce ƙasar ce ta fi kowacce yawan masu cutar a yammacin Afirka, kuma an daɗe ana samun kiraye-kiraye daga faɗin duniya na ganin Najeriya ta zage damtse wajen yaƙi da yaɗuwar cutar.