Za’a iya shafe shekaru masu yawa ba’a magance kalubalen tsaro ba a Arewa maso yamma – Sultan

0 196

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Saad Abubakar III, ya ce za a iya kwashe sama da shekaru masu yawa kafin yankin Arewa maso Yamma ya iya magance kalubalen tsaro da kakkabe da ‘yan bindigar da suka addabi yankin.

Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta kasa (NSCIA) ya bayyana haka a taron zaman lafiya da tsaro da dake gudana a yankin Arewa maso Yamma a jihar Katsina.

Sarkin Musulmi ya bayyana shirin sarakunan gargajiya na yin hadin gwiwa da hukumomin tsaro da gwamnoni bakwai na shiyyar domin ceto yankin daga dimbin matsalolin ‘yan fashi da masu tada kayar baya.

Ya yi imanin cewa a karshen taron, za a samu hanyoyin rage barazanar da ‘yan bindigar ke da shi domin mutane su koma rayuwa ba tare da fargaba ba da kuma gudanar da harkokin kasuwanci.

Taron ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, wanda ya wakilci shugaba Bola Tinubu, da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnoni bakwai na jihohin da ke arewa maso yamma, shugabannin hafsoshin tsaro da kuma sufeto janar na ‘yan sanda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: