Majalisar wakilai ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan matsalolin da suka shafi tafiye-tafiyen alhazan Najeriya zuwa Saudiyya a bana.
Gidan rediyon Sawaba ya ruwaito cewa, a kalla mahajjata 14 ne suka rasu a aikin hajjin bana.
Da yake bayar da karin haske a ranar Lahadin da ta gabata a birnin Makkah yayin taron bitar bayan Arfa, shugaban tawagar likitocin Najeriya mai kula da aikin hajjin bana, Dakta Usman Galadima, ya ce mahajjata bakwai ne suka rasu a lokacin hawan Arfa.
Ya bayyana cewa mutum daya da ya rasa ransa dan jihar Filato ne; sai mutum biyu daga Kaduna; biyu daga Osun; daya daga Borno; daya daga Yobe; daya daga Babban Birnin Tarayya; daya daga Benue; yayin da Legas ke da daya.
Majalisar ta yi nuni da cewa, jimillar ‘yan Najeriya dubu 95,000 ne suka je aikin Hajjin bana. Idris ya shaida wa majalisar cewa akwai jami’an gwamnati da dama da ba su da tanti kuma an sanya su kwana a wurare da yanayi marasa kyau.