Za’a ci gaba da sayar da man fetur a tsohon farashi har sai tsohon kaya ya ƙare

0 56

Ƙungiyar dillalan man fetur ta kasa, IPMAN da kuma kamfanin mai na ƙasa wato NNPCL , sun ce za su ci gaba da sayar da man fetur a tsohon farashi har zuwa lokacin da tsohon kayan da suke da shi zai ƙare.

Kamfanin na NNPCL dai ya ce a sabon farashin zai riƙa bai wa dillalan man a kan naira 899 inda su kuma za su sayar a kan naira 935. Ƙungiyar dillalan man ta ce a yanzu haka tana ci gaba da tattaunawa da matatar mai ta Dangote domin ganin yadda za su soma ɗaukar man a sabon farashin, kamar Alhaji Salisu Ten-Ten, shugaban dillalan na shiyyar arewa maso yamma ya bayyanawa manema labarai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: