Za’a bullo da harajin titi ga masu ababen hawa, Mohammed Nami
Shugaban hukumar tara kudaden shiga ta kasa, Mohammed Nami, ya bayyana cewa hukumar na aiki kan kudirin da zai bullo da harajin titi ga masu ababen hawa.
Mohammed Nami ya ce kudirin zai kunshi amfani da na’u’rori don karban haraji daga masu amfani da tituna don inganta hanyoyin samun kudaden shiga.
Ya bayyana hakan ne a jiya lokacin da ya bayyana a gaban Kwamitin Kudi na Majalisar Wakilai.
A cewar Mohammed Nami, hukumar za ta aika da kudirin ga Majalisar Wakilai ta kasa domin tantancewa da zartar da shi.
Mohammed Nami ya ce duk da cewa Hukumar na shirin tara kudi naira tiriliyan 10 a fadin tarayyar kasarnan a shekara mai zuwa, kudin ba za su wadatar ba wajen gyara dukkanin titunan kasarnan.
An bayar da rahoton cewa majalisar zartarwa ta tarayya, a makon da ya gabata, ta amince da sabuwar dokar tituna.
Manufar dokar ita ce sake dawo da toll gate domin karbar haraji akan titunan kasarnan.