An sake tabbatar wa matasan NYSC cewa za a biya su alawus din N77,000 a karshen watan Maris din nan
Darakta Janar na hukumar matasa masu yi wa kasa hidima NYSC Brig Gen Olakunle Oluseye Nafiu ya tabbatar wa da matasan cewa za su samu karin alawus zuwa N77,000 daga N33,000 a watan nan na Maris.