Za’a bada bashi ga kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa a Najeriya

0 298

Ofishin mataimakin shugaban kasa hadin gwiwa da bankin masana’antu, zasu fara bada bashi ga kanana da matsakaitan ‘Yan kasuwa a fadin kasar nan, a cikin watan Janerun shekarar 2024.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan samar da ayyuka, da kanana da matsakaitan ‘Yan kasuwa na ofishin mataimakin shugaban kasa Temitola Adekunle-Johnson,shine ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja.

Mista Adekunle-Johnson, yace wannan wani kokari ne na gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na taba tallafi da taimakawa kanana da matsaikatan ‘Yan kasuwa a fadin kasar nan.

Ya bayyana cewa za’a raba bashin Naira Bilyan 75 ga kanana da matsakaitan ‘Yan kasuwa masu sha’awa da kashi 9 kacal na ruwa. Mista Adekunle-Johnson, bayyana cewa gwamnatin tarayya da bankin masana’antu basu fitar da tsarin bada lamunin ga Mata da Masa masu kananan kasuwanci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: