Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewa za ta samar da cibiyoyi na musamman ga almajirai da masu buƙata ta musamman domin yin buɗa baki a lokacin azumin Ramadan.
Gwamnan ya bayyana haka ne a sa’ilin da ya ƙaddamar da wani sabon masallacin juma’a.
Ya ce “mun ci alwashin faɗaɗa cibiyoyin buɗe-baki zuwa wuraren da babu su domin amfanin mabuƙata a cikin al’umma.
Ciyarwa a lokacin azumin Ramadana wani abu ne da yawancin jihohin arewacin Najeriya ke gudanarwa a kowace shekara, sai dai batu ne da ke janyo muhawara sanadiyyar maƙudan kuɗaden da ake kashewa.
Yayin da wasu ke kallon lamarin a matsayin tallafawa wa al’umma, wasu na ganin cewa za a iya amfani da kuɗaɗen wajen aiwatar da ayyukan gwamnati waɗanda za su amfani al’umma.