Gwamnatin Jihar Bauchi ta sanar da shirinta na gudanar da kidayar gano hakinanin adadin masu sana’ar karuwanci a Jihar domin samun duk wasu tabbatattun bayanai a kansu.
Malam Aminu Balarabe Isah, Kwamishinan dindindin a Ma’aikatar Hisbah da Shari’a ne ya bayyana hakan yayin wani taron wayar da kan masu sana’ar karuwanci da aka gudanar ranar Litinin a Bauchi.
A cewarsa, tattara bayanan zai taimaka wa hukumar wajen daukar matakan da za su yi kasa a gwiwa da kuma zare musu sha’awar ci gaba da wannan mummunar sana’a mai cike da hadari.
Kwamishinan ya ce, daga cikin ababen da gwamnatin Jihar za ta aiwatar domin cimma wannan nufi akwai shirin bayar da tallafi da kuma sama musu jari na shiga kasuwanci domin samun abin dogaro da kai.
Ya bayyana cewa, binciken da suka gudanar ya nuna cewa mafi akasari matan sun shiga sana’ar karuwanci ne sakamakon rashin ilimi, talauci ko kuma azabtarwa da suka rika fuskanta a wajen iyayensu mata musamman kishiyar uwa.
Ya ce, kananan rikice-rikice a cikin dangi suna kuma taka rawar gani wajen jefa wasu matan cikin wannan mummunar sana’a, lamarin da ya bayar da tabbacin cewa gwamnati za ta yi bakin kokarinta wajen mayar da su wurin iyayensu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito Malam Balarabe yana cewa, gwamnatin jihar ta kuma kudiri aniyar aurar da su ga duk wacce ta samu wanda ya nuna sha’awar aurenta da gaske.
Hafsat Azare, wadda ta yi magana a madadin sauran karuwan, ta bayar da tabbaci kan shirinsu na watsi da wannan sana’a madamar gwamnati za ta tallafa musu, inda ta bayyana halin da suka tsinci kansu a yanzu a matsayin abin a tausaya.