Za a shirya horaswa ga dukkan alkalan kotunan majistire akan hukunta masu laifi a jihar Jigawa

0 130

Hukumar kula da harkokin shari’a ta jihar Jigawa za ta shirya horaswa ga dukkan Alkalan kotunan majistire akan hukunta masu laifi ta hanyar saka su aiki, ba tare da zaman gidan kaso ba.

Babban Alkalin Jiha kuma Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan Shari’a, Mai Shari’ah Umar M. Sadiq ne ya bayyana hakan a lokacin da Shugaban Hukumar Gyaran Da’a na Jihar Jigawa ya kai masa ziyara a ofishinsa da ke Dutse.

A cikin wata sanarwa daga Daraktan Ayyuka na Musamman, Abbas Rufa’i Wangara, Babban Alkalin ya bayyana hukunta masu laifi ba tare da zaman gidan kaso ba a matsayin mafi kyawun hanyar ladabtarwa da rage cunkoson a gidajen gyaran da’a.

Babban Alkalin ya bayyana cewa akwai kyakkyawar alakar aiki tsakanin bangaren shari’a da hukumar gidajen gyaran da’a.

Da yake magana tun da farko, Shugaban Hukumar Gyaran Da’a na Jihar Jigawa, Mu’azu Garba Charanchi, ya bayyana gamsuwa bisa hadin kai da goyon bayan da suke samu daga bangarorin zartarwa da na shari’ah na jiharnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: