Za a Dawo da karbar haraji kan gidajen haya da Takardar shaidar mallakar gidaje

0 198

Hukumar tattara kudaden haraji ta kasa ta bayyana sabbin matakan tattara kudade wadanda zasu taimaka wajan rage Baraka da zarge-zargen da ake yiwa wadansu Ma’aikatanta domin samun kudaden shigar hukumar.

Hukumar ta bayyana cewa daga yanzu ya zama wajibi ake biyan kudin harajin gidajen haya dana takardun mallakar gidaje.

Wannan sanarwar ta fito daga bakin daraktan yada labarai na hukumar Mr Abdullahi Ahmad, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a babban birnin tarayya Abuja.

Inda ya bayyana cewa wannan sabon tsarin yazama wajibi kuma za’a sanya shi a cikin doka, domin tabbatar da cewa kowa ya biya.

Sannan Ahmed ya tabbatar da cewa duk takardun shaidar da mutum ya biya, zasu kasance a kundin tarihin Ajiyar da cire kudaden hukumar.

Kaza-lika, ya kara da cewa sabon tsarin zai taimakawa masu kasuwanci da mallakar gidaje da ofis-ofis domin tabbatar ba’a damfare su ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: