Kakar masu yi wa ƙasa hidima wato NYSC za ta yanke saƙa a Najeriya, bayan da gwamnatin ƙasar ta yi alkawarin biyan su cikon alawus mafi ƙaranci na watannin baya da ba a biya su ba.
Ko da yake babu takamaiman ranar da za a fara biyan matasan masu yi wa ƙasa hidima, amma ministan ci gaban matasa, Ayodele Olawande ya bayar da tabbacin biyan cikon a lokacin da yake magana da gidan talabijin na Channels a ranar Talata.
Tun a watan Satumban 2024 ne gwamnatin ƙasar ta amince da biyan su sabon alawus mafi ƙaranci na naira 77,000 daga naira 33,000 da ake biyan su, sai dai kawo yanzu ba su kai ga cin gajiyar ƙarin ba.
Haka kuma a watan Maris da muke ciki ne ake sa ran masu yi wa ƙasa hidimar za su fara ƙarban sabon alawus din.
Hakan na zuwa ne yayin da miliyoyin ƴan ƙasar ke fama da tsadar rayuwa sakamakon hauhawar farashin kayayyaki saboda janye tallafin man fetur da wasu manufofin da gwamnati ta fito da su.
Lamarin da ya sa wasu masu sharhi ke ganin ƙarin alawus ɗin bai taka kara ya karya