A jiya ne majalisar wakilai ta kasa ta umarci kwamitinta na ayyuka ya binciki watsi da sashe na 1 na aikin hanyar Kano zuwa Maiduguri da ‘yan kwangilar da aka bawa aikin.
Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da Yusuf Shittu Galambi ya gabatar inda ya tunawa majalisar cewa gwamnatin tarayya ta amince da kwangilar kammala aikin titin tun a watan Oktobar 2006.
Ya ce titin Kano zuwa Maiduguri babbar hanyar ce ta hada Jihohin kasar nan da suka hada da Kano, Jigawa, Bauchi, Yobe da kuma Borno.
Shittu ya ce an bayar da kwangilar gina sashe na 1 na aikin ga kamfanin Dantata and Sawoe Construction Company Nigeria Limited. Majalisar ta amince da kudirin kuma ta mika shi ga kwamitinta na ayyuka domin ya gudanar da bincike tare da bayar da rahoto cikin makonni uku domin daukar matakin doka.