Yusuf Falgore ya zama sabon shugaban majalisar Kano

0 288

An zabi wakilin Karamar Hukumar Rogo, Yusuf Ismail Falgore a matsayin sabon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Haka kuma, an zabi wakilin Rimin Gado da Tofa Muhammad Bello Butu-Butu a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar.

Wadannan sabbin shugabanni dai su ne za su maye gurbin tsoffin shugabannin majalisa ta 9, wato Hamisu Chidari da kuma Kabiru Hassan Dashi.

An ruwaito cewa, a yau Talatar ne akayi zaben shugannin majalisu a jihohi daban-daban da kuma a matakin tarayya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: