“Yunwa zaka kashe mu”, a cewar mazauna yankin da akai kulle a jihar Filato

0 291

Dokar hana fita da gwamnatin jihar Filato ta sanya a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da Bassa na ci wa mazauna yankin tuwo a kwarya yayin da mafi yawansu a jiya suka koka bisa karancin abinci.

Manema labarai sun bayar da rahoton cewa tsakiyar birnin ya zama wayam kuma jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ‘yan sanda da ‘yan banga suna sintiri a manyan tituna don tabbatar da bin umarnin gwamnati.

Gwamnan jihar a ranar Lahadi da yamma ya sanar da dokar hana fita bayan ya fahimci yiwuwar rikici a birnin Jos bayan harin da aka kai kan matafiya wanda ya yi sanadin mutuwar 27 daga cikinsu sannan da yawa daga cikinsu sun ji rauni yayin da har yanzu aka nemi 10 aka rasa.

Matafiyan na kan hanyarsu ta komawa jihohin Ondo da Ekiti bayan halartar wani taron addini a Bauchi.

Amma da yake zantawa da manema labarai kan tasirin dokar hana fita a kananan hukumomin, wani mazaunin birnin mai suna Isaac Abraham, ya ce dokar hana fita na damunsu sosai kuma yana kiran da a sake duba ta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: