Yawan al’ummar kasar China ya sake raguwa a shekara ta biyu a jere

0 215

Yawan al’ummar kasar China ya sake raguwa a shekara ta biyu a jere Alkaluma sun nuna cewa an samu raguwar yawan mutane miliyan biyu a bara fiye da ninki biyu na raguwar da aka samu a shekara ta 2022.

An kuma samu ƙarin mace-mace da galibi ake alaƙanta wa ga annobar korona.

Halin da ake samu na yawan tsofaffi a al’ummar ƙasar ya sa gwamnatin China ta buƙaci iyalai da su ƙara yawan yaran da suke haifa. A shekarar da ta gabata ne wani ƙiyasi na Majalisar Ɗinkin Duniya ya nuna cewa ƙasar Indiya ta wuce China a matsayin ƙasa mafi yawan al’umma a duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: