Yau ake cika shekaru 10 da zanga zangar da ta kawar da shugaban kasar Burkina Faso

0 161

Yau ake cika shekaru 10 da zanga zangar da ta kawar da shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore daga karagar mulki bayan ya kwashe shekaru 27 a karagar jagorancin kasar.

Wasu fusatattun matasa da kuma ‘yan siyasa ne suka kaddamar da zanga zanga a ranar 21 ga watan Oktobar shekarar 2014 lokacin da shugaban kasar Burkina Faso Balaise Compaore ya kudiri aniyar amfani da majalisar dokokin kasa domin sauya kundin tsarin mulkin kasar da zai ba shi damar ci gaba da zama a karagar mulki.

Zanga zangar ta fara kazanta daga ranar 28 ga wata zuwa 31 ga wata, lokacin da matasan suka kutsa kai majalisar dokoki suka kuma banka mata wuta domin nuna fushinsu. Wannan zanga zangar ta tilastawa Compaore tserewa ya bar Burkian Faso, abinda ya kawo karshen mulkinsa na shekaru 27 bayan juyin mulkin da ya yi wajen hallaka abokinsa kuma fitaccen shugaban kasa Thomas Sankara da ya yi farin jini a Afirka a kan manufofinsa na ci gaban nahiyar

Leave a Reply

%d bloggers like this: