Yau Talata ake bikin rantsuwar kama aikin sabon shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye, wanda zai maye gurbin shugaba mai barin gado Macky Sall da ya shafe tasawon shekaru 12 ya na mulkin kasar ta yammacin Afrika, tun daga shekarar 2012 zuwa 2024.
Shugabannin kasashe daga ciki da wajen nahiyar Afirka ne ke halartar taron bikin rantsuwar kama aikin sabon shugaban kasar na Senegal mai shekaru 44, cikinsu kuma har da shugaban kasa, kuma shugaban kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS Bola Ahmed Tinubu.
A yayin da sabon shugaba Bassirou Diomaye Faye ke kama aiki daga yau Talata, masu bibiyar lamurran Senegal ciki da wajenta na cigaba da tofa albarkacin bakinsu akan manufofin da suke fatan sabon shugaban zai gabatar, da kuma tarin kalubalen da ke gabansa na kawar da wasu matsaloli da ke ci wa kasar tuwo a kwarya.