‘Yansand sun tabbatar da kama wani manomi bisa zargin sanya guba a rijiyoyi 9 a wani kauye

0 242

‘Yansanda a jihar Yobe a yau sun tabbatar da kama wani manomi dan shekara 25, mai suna Mohammad Mohammad, bisa zargin sanya guba a rijiyoyi 9 na kauyen Kasesa dake kusa da Damaturu, babban birnin jihar.

Kakakin yansanda na jihar, Dungus Abdulkarim, ya sanar da haka a wata ganawa da kamfanin dillancin labarai na kasa.

Dungus Abdulkarim yayi bayanin cewa wanda ake zargin ya zuba maganin kwari cikin rijiyoyi 9, wadanda a su ake samun ruwa domin mazauna kauyen da makiyaya.

Kakakin na yansanda yace wanda ake zargin ya amsa laifinsa, amma yace aniyarsa shine hana makiyaya mamaye gonarsa.

Dungus Abdulkarim yace rundunar yansanda na kokarin kama makiyayan tare da tuhumarsu da laifin kutse cikin gonaki.

Ya shawarci manoma da makiyaya su guji aikata abubuwan da ka iya tayar da rikici.

Leave a Reply

%d bloggers like this: