‘Yansandan jihar Jigawa sun kama wani mutum da ya cakawa matarsa adda har ta mutu a karamar hukumar Babura

0 335

‘Yansanda a jihar Jigawa sun kama wani mutum dan shekara 35 mai suna Abdulmumini Abdullahi, bisa zargin cakawa matarsa mai shekara 25 adda, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwarta a yankin karamar hukumar Babura ta jiharnan.

Kakakin ‘yansanda na jiha, ASP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da kamen cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse.

Shiisu Adam yace an kama wanda ake zargin bayan ‘yansanda sun samu wani labari a ranar 2 ga watan Satumba cewa ya tare matarsa mai suna Sahura Sule inda ya kasheta akan hanyar zuwa daji.

Yayi bayanin cewa bayan samun labarin, ‘yansanda sun ziyarci inda abun ya faru kuma suka dauki marigariyar zuwa babban asibitin Babura.

Ya bayyana cewa an samu marigariyar da saran adda a cikinta da kafadarta ta dama, kuma wani babban likita ya tabbatar da mutuwarta.

Ya kuma sanar da cewa an mika gawar ga iyalanta domin binneta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: