Yan Tada Kayar Baya Sun Sako Sojojin Jamhuriyar Tsakiyar Africa 19
Kungiyar baga agaji ta kasa da kasa Red Cross, tace yan tada kayar baya sun sako sojojin jamhuriyar tsakiyar Afrika 19 da sukayi garkuwa dasu.
Kungiyar tace masu tada kayar bayan sun sace sojojin a arewacin kasar, yayin da suke dab da zuwa wani gari Birao kafin a tura su zuwa babban birnin kasar nan Bangui.
A watan da ya gabata yan tada kayar bayan aka zarge su da kai farmaki wata mahakar ma’adanai inda suka kashe yan kasar chana 9 dake aiki a wurin.
Yan tada kayar bayan suna zargin sojojin hayar Wagner mallakar kasar Rasha da taimakawa gwamnatin kasar wajen murkushe su.