Yan sandan Jihar Jigawa sun kama mutum 14 da ake zargi da satar shanu da wasu miyagun laifuka

0 305

Rundunar Yan sandan Jihar Jigawa ta kama wasu mutane 14 da ake zargin su da satar shanu, saida kwaya, sata da kuma tada zaune tsaye.

Kazalika, an kwato mota guda daya da babur, da dan maraki, awakai guda uku da kuma miyagun kwayoyi a hannun su.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin yan sandan jihar Jigawa DSP Lawan Shisu ya rabawa manema labarai jiya a Dutse.

Sanarwar tace dakarun yan sandan na karamar hukumar Jahun yayinda suka fito aiki a hanyar Gujungu, sun kama wani mai suna Yakubu Abubakar dan shekaru 30 dan asalin Kauyen Kadowawa dake karamar hukumar Jahun, sai kuma Ibrahim Buba mai shekaru 25 dan Kauyen Ganuwar Kore dake karamar hukumar Kafin Hausa da awakai uku dake kyautata zaton na sata ne. Wadanda ake zargin sun amsa laifin satar dabbobi a karamar hukumar Kiyawa da Kafin Hausa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: