Rundunar ƴan sanda a jihar Zamfara ta ce jami’anta sun tarwatsa wani yunƙurin ƴan bindiga na kai hari a wani ƙauye da ke yankin ƙaramar hukumar Tsafe.
Haka nan jami’an sun samu nasarar hallaka ƴan bindigan guda biyu.
A cikin wata sanarwa da fitar mai dauke da sa hannun kakakin rundunar a jihar, Mohammed Shehu, ta ce lamarin ya faru ne jiya Lahadi, inda aka yi artabu tsakanin jami’an ƴan sandan da kuma maharan.
Sanarwar ta ce baya ga waɗanda aka kashe, wasu maharan sun tsira da munanan raunuka.
- Comments
- Facebook Comments