‘Yan Sanda Sun Kama Masu Satar Mutane A Wani Hadin Gwiwa Da ‘Yan Gari a Kaduna

0 206

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Muhammad Jalige, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna.

“Rundunar tana fadawa jama’a cewa, ba zata yi kasa a gwiwa ba wurin dakile ayyukan miyagu da masu garkuwa da mutane da masu satar shanu da kuma masu fashi da makami a cikin jihar da kuma nasarori da rundunar ta samu,” inji Jalige.

A cewarsa, a ranar 26 ga watan Maris, da misalin karfe 12 na dare rundunar ta samu labarin wasu ‘yan bindiga su goma dauke da muggan makamai sun tare hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari inda suka yi yunkurin garkuwa da wasu mutane biyar da ke cikin wata mota kirar golf bokswaja (Volkswagen Golf), dake kan hanyarta zuwa Birnin Gwari daga Kaduna.

Ya ce “da samun wannan labari, rukunin jami’ai masu sintiri a tashar ‘yan dake Buruku ya gaggauta daukar mataki inda suka yi musayar wuta kana su ka yi nasarar tarwatsa ‘yan bindigan suka ceto mutanen da ke cikin motar babu abin da ya taba lafiyar su.

An yi kokarin tabbatar da ganin an kamo ‘yan bindigan da suka arce,” inji shi.

Mai Magana da yawun ‘yan sandan ya ce tuni aka mika mutanen da aka ceto ga iyalan su.

Jalige ya kuma fada cewa, a wannan ranar 26 ga watan Maris, jami’an su sun kama wani da ake zargi da sayar da makamai, aka kuma kwato bindigogin SMG guda takwas da pitol guda da kuma harsasai guda 85 a cikin dajin Saminaka da ke karamar hukumar Lere a jihar.

Ya ce an kaddamar da bincike a kan batun kana sauran wadanda ake zargin sun tabbatar da zasu kai makaman da harsashan ne ga ‘yan bindiga a jihohin Neja da Kaduna da Zamfara da kuma Katsina.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kuma bayyana cewa, a wannan rana kuma wasu masu bincike sun kama masu satar shanu su biyu da shanu 32 da suka sato da awaki 10 a kauyen Ladduga a karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna.

Ya fada cewa samun wannan nasara ba zai rasa alaka da sabon yunkuri na hadin gwiwar ‘yan sanda da unguwanni ba, ta hanyar bada bayanan sirri cikin gaggawa.

Rundunar ‘yan sanda ta gamsu da wannan kyakkyawar gudunmuwa kana ta yi kira ga kowa da ya taimakawa ‘yan sanda a wannan fanni, yayin da itama take tabbatar musu da cikakken rufin asirinsu yayin da zasu bada bayanan sirri.

A kokarinsa don tabbatar da ci gaba da samun nasara a yaki da miyagun ayyuka a jihar, Kwamishinan ‘Yan sanda a jihar, (CP) Umar Muri, ya bukaci jami’ansa da ma’aikata su hada kai da mazauna unguwanni domin samun nasarar dakile hare haren miyagu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: