Yan sanda sun gano gawar almajiri da aka cire masa kai a jihar Jigawa

0 197

Rundunar yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da tsintar gawan wani almajiri dan shekara goma sha huɗu (14) a gefen hanya wanda ya bata tsawon kwanaki biyu ba’a ganshi ba.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Jigawa Shi’isu lawan adam ya tabbatar da faruwan wannan mummunar ta’asa.

Shi’isu yace an tsinci gawar almajirin me suna Bashir Adamu dalibin malam Musa wada a kauyen jikas-dabaja dake karamar hukumar gwaram bayan an yanke masa kai da kuma al’aurar sa.
Hukumar ta bada gawar sa wa masu ita domin yi masa sutura.
Ya kara da cewa tuni dai shugaban rundunar yan sandan jihar AT Abdullahi ya bada umarnin binciko wadanda sukayi wannan danyen aikin domin karbar sakamakon aikin da suka yi.

Leave a Reply