Rundunar yansandan jihar Jigawa ta kame mutane 20 da take zargi da aikata laifuka daban-daban da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane da kisan kai, inda ta kwato kayan sata daga hannunsu da kuma makamai.
Kwamishinan yansanda na jiha, Usman Sule Gomna, ya sanar da haka a taron manema labarai a Dutse.
Kwamishinan ya bayyana cewa tawagar yansanda ta musamman masu yaki da fashi da makami sun kai farmaki kan wasu maboyar ‘yan fashi a yankin karamar hukumar Ringim inda suka damke wasu daga cikin ‘yan fashin.
- Mutane da dama sun mutu bayan da wani jirgin sama ya yi hatsari a Kazakhstan
- Gwamnan Kebbi ya bada motocin shinkafa guda 3 don bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara
- Gwamnatin jihar Jigawa ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000 a jihar
- Nijeriya ba ta cikin jerin ƙasashen da suka fi dogaro da lamuni daga IMF a Afirka
- Gwamnatin Tarayya ta wanke mutane 888 daga zargin ta’addanci
Ya kara da cewa jami’an yansanda a karamar hukumar Babura sunyi arangama da wasu yan bindiga 9 a kauyen Andau dake yankin karamar hukumar.
Sule Gomna ya kuma ce tawagar yansanda ta musamman masu yaki da fashi da makami sun kama mutane 10 da ake zargin barayine yan bindiga a kwaryar birnin Dutse.