Yan Mata 717 Sun Shaki Iska Mai Guba A Iran

0 148

Rahotanni daga Iran na cewa ƴan mata a makarantu da dama da ke ƙasar sun shaƙi iska mai guba bayan komawarsu makaranta a wani lamari mai ban mamaki da ya girgiza ƙasar.
Wani likita ɗan Iran yake cewa cikin kwanaki biyun farko bayan ɗalibai sun koma makaranta, kimanin ɗalibai mata ɗari bakwai da goma sha bakwai aka kai wa hari.
Hotuna da bidiyo sun nuna yadda gurbatacciyar iskar ta yi wa ɗaliban illa a makaratu da ke Khuzestan da Ardabil da Urmia.
Hukumomi sun ƙaddamar da bincike inda jagoran addini Ayatollah Ali Khamenei ya ce ya kamata a yanke hukunci mai tsanani ga waɗanda aka samu da laifi.
Sai dai Iraniyawa suna ganin hukumomi na da hannu a lamarin.
A wani labarin kuma, Hukumomin Iran sun fara kafa kyamarori a wuraren da mutane ke taruwa domin gano matan da ke yawo ba tare da hijabi ba, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana.
Duk macen da aka samu ba ta sanya hijabi ba za a aika mata saƙon jan kunne a cewar hakumar ‘yan sanda.
Zanga-zanga ta mamaye Iran a bara, bayan an zargi ‘yan hizba da sanadin mutuwar wata matashiya mai suna Mahsa Amini, wata Baƙurdiya da aka zarga da karya dokar sanya hijabi.
Tun bayan mutuwar Mahsa, mata da yawa ke sanya hijabi musamman waɗanda ke zaune a manyan birane.

Leave a Reply

%d bloggers like this: