Yan kungiyar asiri sun kashe mutum bakwai lokacin wani hari a jihar Imo
Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne sun kashe mutane bakwai lokacin wani hari a kauyen Mmaashu a yankin karamar hukumar Ohaji ta jihar Imo.
Kakakin yansanda na jihar, Micheal Abbatam, wanda ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa yau da rana, yace ‘yan bindigar da suka rufe fuskokinsu, da yawansu ya kai 20, suna karkashin jagorancin wani mai suna Ossy, mutumin da ya tsere daga gidan gyaran hali na Imo, babban birnin jihar ta Imo.
Yace binciken farko da ‘yansanda suka yi, ya bayyana cewa kashe-kashen na da alaka da kungiyar asiri.
Kakakin yansandan yace jagoran kungiyar, Ossy, ana zarginsa da kasancewa dan kungiyar asiri, yayin da mutanen da aka kashe, ake zargin ‘ya’yan wata kungiyar asirin da basa ga maciji da juna.
Yace kwamishinan ‘yansanda na jihar, Rabiu Hussaini, ya umarci mataimakin kwamishinan yansandan mai kula da shashen bincike da ya gaggauta kaddamar da wani binciken sirri bisa lamarin da nufin kama wadanda suka kitsa shi.