Yan jihar Jigawa 1,350 sun fara karbar horo daga hukumar samar da aiyuka ta kasa

0 223

Hukumar samar da ayyukan yi ta kasa ta fara bayar da horo ga matasa dubu 1 da 350 a jihar Jigawa.

Jagoran hukumar na jiharnan, Malam Abubakar Jamo, ya sanar da haka a wata ganawa da kamfanin dillancin labarai na kasa a Dutse.

Abubakar Jamo yace aikin horon na watanni 3 wanda aka fara a wannan watan na Oktoba, za a gudanar da shi a karkashin shirin hukumar na koyar da sana’o’in hannu.

Yayi bayanin cewa an zabo mutane 50-50 daga kowace karamar hukuma cikin kananan hukumomin jiharnan 27 domin cin gajiyar shirin.

Abubakar Jamo ya kara cewa za a bayar da horo akan gyaran mota da dinki da gyaran injinan wuta da aikin komfuta da kafinta da gyaran wayar hannu da aikin jima da aski da kuma zane-zane.

Jagoran yayi nuni da cewa za a bayar da horon ne da nufin rage zaman kashe wando tsakankanin matasa a jiharnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: