‘Yan Gudun Hijira Sun Koka Kan Rashin Abinci Da Sauran Bukatu A Jihar Neja

0 113

Yan gudun hijirar da ke garin Kafin-Koro ta karamar hukumar Paikoro a Jihar Neja sun koka kan rashin abinci da sauran bukatu da suka hada da tufafi a sansanin.

Yan gudun hijirar sun fito ne daga al’ummomi daban-daban da suka hada da Adunu, Beni, Kabula, Zazzaga, Kazai, Fuka, Nanati da kuma karamar hukumar Kwagana dake jihar.

An shaida wa wakilinmu cewa wani yaro dan shekara daya mai suna Christopher Yusuf, wanda aka yi garkuwa da mahaifiyarsa tare da wasu da dama a ranar 14 ga watan Maris a garin Adunu da ke karamar hukumar Paikoro ya kamu da cutar kwashiorkor. Mazauna yankin sun ce jaririn ana shayar da shi da shayi da madarar roba amma ba kasafai yake karba ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: