‘Yan daba dauke da makamai a yau sun tarwatsa zaben cike gibi a mazabun Alasawa da Kwaciri dake karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.
An bayar da rahoton cewa ana gudanar da zaben domin kammala zaben ‘yan majalisar wakilai na ranar 25 ga watan Fabrairu wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana cewa bai kammalu ba.
Amma a mazaba ta 30 dake Kurna Gabas, wasu ‘yan daba dauke da muggan makamai wadanda yawansu ya kai daruruwa sun mamaye akwatunan zabe tare da tarwatsa masu kada kuri’a.
An bayar da rahoton cewa ‘yan dabar sun lalata wani akwatin zabe yayin da suka kasa samun nasarar kwace sauran ukun.
Wani shaidar gani da ido ya bayar da rahoton cewa ‘yan dabar sun zo dauke da muggan makamai kuma suka tarwatsa masu zabe, inda ya kara da cewa daya daga cikin ‘yan dabar ya fasa daya daga cikin akwatunan zabe guda 4.
A cewarsa an samu ceto sauran akwatunan zabe bayan samun daukin gaggawa daga ‘yansanda wadanda suka raraka ‘yan dabar kuma suka kwashe akwatunan da sauran kayayyakin zabe zuwa ofishin ‘yansanda na Kurna.
- Comments
- Facebook Comments