Yan Boko Haram sun kai sabon hari a karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe

0 234

Wasu mahara da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kaddamar da hari a garin Babbangida, hedkwatar Karamar Hukumar Tarmuwa, a Jihar Yobe.

Wata majiya a yankin ta tabbatar da cewa mayakan na can suna musayar wuta da dakarun sojojin da ke yankin.

A cewar majiyar, tuni mazauna yankin da dama suka fantsama cikin dazuka don tsira da rayukansu.

Harin dai na zuwa ne bayan an dan sami sassaucin yawan kai hare-haren mayakan Boko Haram da na ISWAP a yankin Arewa maso Gabas a ’yan kwanakin nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: