‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wani manajan bankin TAJ reshen jihar Zamfara

0 277

Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wani manajan bankin TAJ reshen jihar Zamfara, Mansur Kaura, a safiyar jiya Talata.

Wani mazaunin yankin mai suna Musa Ibrahim ya ce an yi garkuwa da Mansur Kaura ne a lokacin da ‘yan bindigan suka kai farmaki gidansa da ke unguwar Rijiyar Gabas a Gusau, babban birnin jihar Zamfara da misalin karfe 1 na safe.

Da yake magana game da sace manajan bankin a Gusau, Ibrahim ya ce ‘yan bindigar bayan sun yi awon gaba da shi, ba’asan inda suka shi ba.

Ya bayyana  yadda mutanen garin ke komawa gidajensu, babu wanda ya kai masa dauki.

An kasa samun Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Yazid Abubakar, har lokacin hada wannan rahoto.

Leave a Reply

%d bloggers like this: