Yan bindiga sun nemi kudin fansa Naira 200M a jihar Neja.

0 186

Yan bindiga sun nemi kudin fansa Naira Milyan 200 domin sakin wasu manoma 56 da suka yi garkuwa dasu a kauyukan Adunu da Kwagana dake karamar hukumar Paikoro a jihar Neja.

Manema labarai sun rawaito cewa wadanda aka sace din sun shafe kimanin sati uku a hannun wadanda suka sace su da suka hada maza da kuma kananan yara.

Mazauna yankin sun bayyana cewa yan bindigar sun kira waya domin sanar da kashe daya daga cikin wanda sukayi garkuwa dashi, suna kuma barazanar kara kashe wasu muddin ba’a biya kudin fansa ba.

Yan bindigar sun garkuwa da kimanin mutane 100 amma kuma wasu sun kubuta daga hannun su.

Kwamishin tsaro da harkokin cikin gida da bada agaji na jihar Emmanuel Umar bai ce komai ba gangane da faruwa lamarin Kazalika shima shugaban karamar hukumar Paikoro Aminu Umar Yandayi bai amsa kiran da yan jarida suka masa dangane da lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: