‘Yan bindiga sun kashe mutane 4 tare da sace wasu 50 a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara

0 361

‘Yan bindiga sun kashe mutane 4 tare da sace wasu 50 a garin Goran Namaye dake yankin karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

Kakakin rundunar yansandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya sanar da haka ga manema labarai yau a Gusau.

Muhammad Shehu, yace maharan, wadanda suka zo da yawansu, sun mamaye garin da misalin sha biyun daren jiya, inda suka kashe mutane 4 tare da sace wasu 50.

Sai dai, yace an aika da tawagar bincike ta yansanda zuwa wajen.

A cewarsa, kwamishinan yansanda na jihar Zamfara, Yakubu Elkana, ya bayar da umarnin bincike da gano mutanen da aka sace.

Muhammad Shehu ya kara da cewa kwamishinan ya bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankulansu, kasancewar rundunar tana aiki tare da sauran hukumomin tsaro wajen dawo da doka da oda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: