Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki garin Ejule da ke karamar hukumar Ofu a jihar Kogi, inda suka kashe mazauna garin.
An bayyana cewa harin ya fara ne da misalin karfe 3 na safiyar yau Alhamis, an kashe wani dan achaba, da matar wani shugaban matasa a unguwar a harin.
Sannan an ba da rahoton cewa ‘yan bindigar sun kona wani gidan a garin.
Mai baiwa gwamnan jihar Kogi shawara kan harkokin tsaro Kwamanda Jerry Omadara (mai ritaya), ya abbatar da faruwar lamarin a wata hira da manema labarai, amma ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani ba.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar, SP William Aya, bai amsa kiran sa ba lokacin da aka tuntube shi. A halin da ake ciki kuma, rahoton da aka samu da misalin karfe 9:30 na safe ya nuna cewa wasu mutane na cikin gida yayin da wasu kuma suka tsere daga garin.